Isra’ilaTa Kashe Wani Bafalasdine Matashi A Wani Hari Da Takai A Arewacin Kogin Jodan.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Isra’ila sun karbe wani matashi bafalasdine a wani samame da suka kai a cikin dare a wani gari dake Arewacin

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Isra’ila sun karbe wani matashi bafalasdine a wani samame da suka kai a cikin dare a wani gari dake Arewacin gabar yammacin kogin Jodan da isara’ila ta mamaye, wani mazaunin yankin yace sojojin na cin karensu ba babbaka a yankin.

Kamfanin dillancin labaran yankin falasdinu WAFA ya sanar cewa sojojin isara’ila sun bude wuta kan wani yaro matashi dan shekaru 16 da haihuwa Mohammad iyad  a arewa masu yammacin garin jenin inda anan take yace ga garunku nan.

Yan sa’oi kafin afkuwar lamarin sojojin Isra’ila sun farma garin inda suka fara binciken gida-gida tare da harbe-harbe da harsashi mai rai, da kuma wurga gurneti, lamarin da ya jawo mayar da martani daga al’ummar garin,

Kungiyar bada agaji ta yankin falasdinu ta ce wani ma’aikacinta guda daya dan shekaru 30 da haihuwa ya jikkata bayan da sojan isra’ila ya harbe shi da harsashi mai rai a kafarsa kafin daga bisani aka yi Asibiti da shi domin yi masa magani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted