Kungiyar “Oil Change International” mai zaman kanta ta bayyana cewa da akwai kasashe 25 da su ne su ka rika sayar wa da “Isra’ila” man fetur a tsawon lokacin yakin Gaza.
Rahoton wannan jaridar ya yi ishara da kasashe 25 da su ne madogarar Haramtacciyar Kasar Isra’ila” wajen samun makamashin da ta rika amfani da shi a motocinta na yakin Gaza.
Jaridar “al-Ahbar” wacce ta buga wannan rahoton da kungiyar “ Oil Change International” mai zaman kanta ta watsa a yayin taron da ake yin a muhalli a kasar Brazil, ta ce; Kasashen Azerbaijan da kuma Kazakhstan ne a gaba da su ka bai wa ‘yan sahayoniya kaso70% na man fetur din da motocinsu na yaki su ka rika amfani da su tun daga watan Oktoba 2023 zuwa2025.
Rahoton ya kuma ce, wadannan kasashen biyu suna da cikakkiyar masaniya akan cewa man fetur din da suke bai wa Haramtacciyar Kasar Isra’ila za a yi amfani da shi ne a yakin Gaza.
A dalilin hakan, kungiyar ta yi kira ga wadannan kasashen da su yi furuci da cewa da su aka yi laifukan yaki a Gza, musamman yi wa mutane kisan kare dangi.
Tun a farkon yakin ne dai kungiyar ta “Oil Change International” ta bai wa kamfanin tattara bayanai na “Data Disk” kwangiyar bibiyar yadda ake jigilar man fetur zuwa Haramtacciyar kasar ta Yahudawa. Kamfanin kuwa ya iya gano an yi jigilar man fetur din har sau 323, da nauyinsa ya kai nauyin ton miliyan 21.1.
Bayan wadannan kasashen biyu da akwai kasashen Rasha, Girka da Amurka a cikin jerin wadanda suke bai wa Haramtacciyar Kasar ta Yahudawa man fetur.