Najeriya: An yi zanga-zangar tir da barazanar Trump

A Najeriya an yi zanga zangar yin Allah wadai da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na daukar matakin soji kan kasar bisa

A Najeriya an yi zanga zangar yin Allah wadai da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na daukar matakin soji kan kasar bisa zargin gwamnatin kasar da kauda kai kan kisan da ake wa kiristoci a kasar.

Masu zanga-zanga a Kano, dake arewacin Najeriya, sun yi Allah wadai da barazanar da kuma yin watsi da ikirarin na Trump na “kisan kiyashin Kiristoci.”

Masu zanga-zangar sun zargi Washington da amfani da addini domin tsoma baki da a cikin harkokin cikin gidan Najeriya, suna gargadin cewa duk wani matakin soja na Amurka zai keta hurumin Najeriya.

A ranar 1 ga Nuwamba, ne Trump ya ce ya umarci Pentagon da ta shirya daukar matakin soji a Najeriya, yana mai ikirarin cewa wannan shiri an yi shi ne don kare Kiristoci.

Sannan ya yi barazanar dakatar da duk wani tallafi ga kasar” idan gwamnatin Najeriya “ta ci gaba da yin biris ga kisan Kiristoci, Kalaman da suka haifar da fushi a fadin Najeriya.

Kungiyoyin fararen hula da masu sharhi kan siyasa sun zargi Trump da yada labaran karya da kuma haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’umma.

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da wadannan zarge-zargen da kakkausar murya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted