Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati

Kafafen watsa labarun Amurka sun ce, kamfanon jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga 1330 a jiya Asabar saboda ci gaba da rufe ayyukan gwamnatin tarayyar

Kafafen watsa labarun Amurka sun ce, kamfanon jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga 1330 a jiya Asabar saboda ci gaba da rufe ayyukan gwamnatin tarayyar kasar dalilin rashin cimma matsaya akan kasafin kudi a Majalisun kasar.

Masu sanya idanu akan kai da komowar jiragen sama ne su ka dakatar da aiki saboda ba za su karbi albashi ba, idan su ka yi aiki alhali ayyukan gwamnati suna a rufe.

Hukumar filayen jiragen sama ta tarayyar Amurka ce ta sanar da cewa masu aikin kula da zirga-zirgar jiragen sama a hasumiyoyin dake cikin filayane jiragen sama 25 sun dakatar da aiki.

Daga cikin garuruwan da tsaikon aikin ya shafa da akwai Chicago, Sanfarancisco, New York, New Rock da kuma Atalanta.

Tashar talabijin din CNN ta ce, adadin tafiyar jiragen saman da aka dakatar ta kai 1900.

Ana hasashen cewa zuwa jibi Talata 14 ga watan nan na Zuwamba za a sami Karin raguwar kai da komowar jiragen saman daga kaso 6% zuwa 10%.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted