Iran da Pakistan sun habaka cinikayyar kan iyaka don karfafa kasuwanci da tsaro

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce faɗaɗa cinikayyar kan iyaka da hadin gwiwar tattalin arziki Tsakanin Iran da Pakistan zai taimaka

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce faɗaɗa cinikayyar kan iyaka da hadin gwiwar tattalin arziki Tsakanin Iran da Pakistan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kuma habaka ci gaban kasashen biyu, yayin da ake kokarin samar da sabbin damammaki don ci moriyar juna a tsakaninsu.

Da yake magana bayan dawowarsa daga ziyarar kwanaki uku da ya kai Pakistan ranar Juma’a, ya ce, “Idan aka habaka kasuwannin kan iyaka kuma ciniki da Pakistan ya ci gaba da bunkasa, to za a magance yawancin matsalolin rashin tsaro da kalubalen kan iyaka tsakanin kasashen biyu, domin mayar da yankunan kan iyaka zuwa cibiyoyin manyan ayyukan tattalin arziki zai rage fasa-kwauri da rashin tsaro, haka nan kuma  zai share fagen samun kwanciyar hankali da kuma amfanin juna.”

Tafiyar, wadda ta fara a ranar Laraba bisa gayyatar Kakakin Majalisar Dokokin kasar Pakistan Sardar Sadiq, ta hada da ganawa da manyan jami’ai kamar Mukaddashin Shugaban kasa kuma Shugaban Majalisar Dattawa Yusuf Raza Gilani, Firayim Minista Shehbaz Sharif, da Babban Hafsan Hafsoshin Soja Asim Munir.

Ya kara da cewa “daya daga cikin manyan manufofin wannan ziyarar ita ce nuna godiya ga jama’a da jami’an Pakistan saboda matsayins da suka dauka  a lokacin yakin kwanaki 12 da gwamnatin Sahyoniya ta kaddamar kan Iran,” yana mai cewa duk inda tawagar Iran ta hadu da jama’a, suna nuna farin ciki game da martani mai karfi da Iran ta mayar ga zaluncin gwamnatin Sahyonya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted