Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa uku a Yammacin Kogin Jordan

Hamas ta yi Allah wadai da kisan na Isra'ila tana mai cewa kisan nasu "ya zama sabon laifi a laifukan da gwamnatin mamaya.

Sojojin Isra’ila sun kashe akalla Falasdinawa uku yayin da suke fadada hare-haren da suke kai wa a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labarai na Falasdinawa WAFA, wanda ya ambato majiyoyin yankin, ya ruwaito cewa sojojin mamayar sun mamaye kauyen Kafr Qud da karfin soja a ranar Talata.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinawa ta bayyana shahidan da sunan Abdullah Muhammad Omar Jalmana, mai shekaru 27, Qais Ibrahim Muhammad al-Baytawi, mai shekaru 21, da Ahmed Azmi Arif Nashti, mai shekaru 29.

Hamas ta yi Allah wadai da kisan na Isra’ila tana mai cewa kisan nasu “ya zama sabon laifi na laifukan da gwamnatin mamaya ta aikata kan mutanenmu a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted