Amurka : Shirin Isra’ila na mamaye yammacin kogin Jordan, barazana ne ga tsagaita wuta a Gaza

Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya yi gargadin cewa amincewar da majalisar dokokin Isra’ila ta yi na samar da kudirorin doka da nufin tsawaita

Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya yi gargadin cewa amincewar da majalisar dokokin Isra’ila ta yi na samar da kudirorin doka da nufin tsawaita ikon Isra’ila a gabar yammacin kogin Jordan “barazana ne ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.

Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka ya shaidawa manema labarai a lokacin da yake shirin tafiya Isra’ila cewa, ” wannan ba wani abu ne da za mu iya ba da goyon baya gare shi ba a wannan lokaci.”

Furin nasa na zuwa ne bayan da majalisar dokokin Isra’ila ta kada kuri’a kan samar da wani kudirin mallake Gabar Yamma da Kogin Jordan a matsayin yankin Isra’ila.

Kudirin wanda wani dan majalisar Isra’ila mai tsattsauran ra’ayi ya gabatar na zuwa ne a daidai lokacin da mataimakin shugaban Amurka JD Vance ke ziyara a kasar domin tattauna batun tsagaita wuta a Gaza.

A watan da ya gabata, Shugaba Trump ya ce ba zai bari Isra’ila ta mamaye yankin ba, wanda Falasdinawa ke kallo a matsayin tasu kasar.

Amurka dai na son a ci gaba da shirin kafa rundunar tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa da kafa sabuwar gwamnati a Gaza da kuma kwance damarar Hamas, wanda ke cikin mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted