Euro-Med ta bukaci bangarori su shiga Gaza domin tattara bayanai kan kisan kiyashin Isra’ila

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-med mai hedkwata a Geneva ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da shiga Gaza ba tare

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-med mai hedkwata a Geneva ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da shiga Gaza ba tare da ‘yan jarida, masu bincike, da masana harkokin shari’a don tattara bayanan kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, Hukumar ta ce, biyo bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a Masar ranar Litinin, “Dole ne duniya ta ga abinda ya kasance a Gaza.”

Kungiyar ta ce a yanzu dole ne a bar duniya ta ga irin barnar da aka yi, wa matsugunai, da kuma haddassa wahalhalun ga bil adama sanadin yakin da Isra’ila ta yi na kisan kare dangi a Gaza, wanda ya kashe kusan mutane 68,000, yawancinsu mata da yara.

“Kafofin watsa labarai na duniya, masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya, kotun ICC, dole ne su sami damar yin amfani da bayanan kisan gillar da Isra’ila ke yi,” in ji kungiyar kare hakkin bil’adama.

A tsawon shekaru biyu na kisan kiyashi, Isra’ila ta katange Gaza, tare da takaita ayyukan jin kai a zirin, da kuma kai hare-hare ta sama da kasa ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya jefa fararen hula cikin mummunan yanayi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted