Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da tsare tsare da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a hukumance, kamar yadda ofishin Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a yau Juma’a.
Wannan dai na zuwa ne bayan ci gaba da tsaikon da aka samu na tsawon kwana daya biyo bayan amincewar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu a ranar Alhamis. Duk da cewa an amince da matakin farko na yarjejeniyar, amma dai Isra’ila ba ta dakatar da hare-harenta a kan al’ummar yankin zirin Gaza, inda a cikin kasa da sa’oi 24 ta kashe Falastinawa akalla 70 da kuma jikkata wasu da dama a yankuna daban-daban na zirin Gaza.
Tun da farko hukumar yada labaran Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, za a dakatar da yakin da zarar yarjejeniyar ta samu amincewar gwamnati. Sharuɗɗan tsagaita wuta sun haɗa da dakatar da duk wasu ayyukan soji, kamar hare-hare ta sama, da harba harsashen bindigogi, da kuma kai hare-hare ta ƙasa a zirin Gaza.