Afirka ta Kudu da Sin sun kara habaka huldar tattalin arziki don tukarar harajin Amurka

Kasashen Afirka ta Kudu da Sin sun kaddamar da wani sabon yunkuri na zurfafa dangantakar tattalin arziki, inda Beijing ta yi alkawarin zuba jari a

Kasashen Afirka ta Kudu da Sin sun kaddamar da wani sabon yunkuri na zurfafa dangantakar tattalin arziki, inda Beijing ta yi alkawarin zuba jari a fannin hakar ma’adinai, makamashi, da ababen more rayuwa. Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Pretoria ke fuskantar matsanancin  matsin lamba daga sabbin harajin da Amurka ta sanya mata wanda ke yin barazana ga damar da ta ke da ita a karkashin dokar bunkasar Afirka da damammaki (AGOA).

Taron bunkasa harkokin kasuwanci na kasashen Afirka ta Kudu da Sin karo na 9, wanda aka gudanar a ranar Talata, ya jaddada aniyar kasashen biyu na karfafa hadin gwiwar tattalin arziki.

A wajen taron, shugaban kungiyar tattalin arziki da cinikayya ta kasar Sin da Afirka ta Kudu Zhang Chaoyang, ya sanar da cewa, an samu babban ci gaba a fannin hakar zinare a yankin  Gauteng.

Kamfanin Gold One, mallakin kungiyar Baiyin Nonferrous ta kasar Sin, zai zuba hannun jari na rand biliyan 4 (dala miliyan 230) cikin ayyukan, wanda ke nuna kwarin gwiwa ga tattalin arzikin Afirka ta Kudu da ke dogaro da albarkatun kasa.

Asusun bunkasa harkokin tattalin arziki da kasuwancin Sin da Afirka ya kuma tabbatar da shirin shiga ayyukan kai wutar lantarki a gashin Afirka ta Kudu, wanda aka tsara don fadada karfin wutar lantarki tare da tallafin kamfanoni masu zaman kansu.

A halin da ake ciki, kamfanonin da ke da alaka da gwamnatin kasar Sin, irin su China State Construction, sun yi alkawarin kara yawan sayayya a cikin gida, da habaka sassan masana’antu da hidima na Afirka ta Kudu.

Mataimakin ministan kasuwanci Zuko Godlimpi ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin wata dama ta samar da “makoma mai fa’ida ga bangarorin biyu,” yana mai jaddada muhimmancin  mayar da hankali ga saka hannun jari a ayyukan more rayuwa, ayyukan makamashi, da karfin masana’antu a Afirka ta kudu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted