Iran Ta Bayyana Shirinta Na Halartar Taron Shekara-Shekara Na Hukumar Makamashin Nukiliya

Cikakkun bayanai kan halartar Iran zuwa taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya na kasar Iran

Cikakkun bayanai kan halartar Iran zuwa taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya na kasar Iran Muhammad Islami ya yi karin haske kan yadda Iran za ta halarci taron shekara -shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.

Mohammad Eslami ya bayyana dangane da cikakkun bayanai na halartar taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA inda ya ce: A gobe ne za a fara taron shekara- shekara na hukumar IAEA karo na 69 a birnin Vienna.

Ya kara da cewa: “Iran zata tsara tare da gabatar da wani kuduri na yin Allah wadai da harin da aka kai kan cibiyoyin nukiliyarta na zaman lafiya a wurin taron.”

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ya ce: “Suna fatan samun cikakken bayani kan abin da ya faru da cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran ta hanyar halartar wannan taro.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted