Ayatullah Khatami Ya Ja Hankalin Kasashen Larabawa Kan Hare-Haren Isra’ila

Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran ya gargadi kasashen Larabawa game da harin da gwamnatin mamayart Isra’ila ke kaiwa kan kasashe Limamin

Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran ya gargadi kasashen Larabawa game da harin da gwamnatin mamayart Isra’ila ke kaiwa kan kasashe

Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya gargadi gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila za ta kai musu hari idan har ta samu iko, yana mai jaddada cewa, hanyar tunkarar haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya ita ce mayar da martani mai karfi kanta.

Limamin Sallar Juma’ar na Tehran ya bayyana a cikin hudubarsa cewa: “A matsayinsa limamin sallar Juma’ar Tehran, yana cewa, kuma dole ne gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya su ji cewa: Idan haramtacciyar kasar Isra’ila ta iko, za ta kai hari gare su, taken Netanyahu shi ne ‘Kafa Babban Isra’ila’ ma’ana daga kogin Nilu zuwa Kogin Yufiretis, kuma yana son kwace wasu sassan kasashe a Masar da Jordan.

Limamin Sallar Juma’ar na birnin Tehran ya kuma yi tsokaci kan harin baya-bayan nan da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan kasar Qatar da hedkwatar kungiyar Hamas, yana mai cewa: Halin wannan yahudawan sahayoniyyar shi ne zubar da jinin bil’adama, kuma an kirkire ta ne shekaru 80 da suka gabata da nufin zubar da jini. Ya kara da cewa: “Kada ku yi shakkun cewa tabbas Amurka na da hannu a wannan aika-aika, sararin samaniyar kasar Qatar yana karkashin sansanin Al-Udeid na Amurka, to ta yaya ba za su sani ba?” Wasu kuma sun ce ya zama wajibi Isra’ila ta aiwatar da wannan farmaki, kuma Trump ya ce ya yi bakin ciki ba don ta kai wa Qatar hari ba, sai don ta gaza, kuma shugabannin Hamas sun tsira.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted