Jagororin Hamas Sun Kubuta Daga Kisan Gillar Isra’ila Ne A Lokacin Da Suka Tafi Yin Sallah

Wani dalili da ba zato ba tsammani ya janyo gazawar kashe manyan shugabannin Hamas a Doha Kafofin yada labarai sun bayyana wani dalili na bazata

Wani dalili da ba zato ba tsammani ya janyo gazawar kashe manyan shugabannin Hamas a Doha

Kafofin yada labarai sun bayyana wani dalili na bazata a ranar Laraba da ya biyo bayan gazawar da Isra’ila ta yi na kashe manyan shugabannin Hamas a Doha babban birnin Qatar. Kamfanin dillancin labaran RT ya nakalto tashar talabijin ta Channel 12 cewa, kwana guda bayan kaddamar da shirin kawar da ofishin siyasa na kungiyar Hamas a birnin Doha, rahotanni na nuni da cewa harin bai yi nasara ba, sakamakon matakin da shugabannin Hamas suka dauka na yin sallar azahar tare da ficewa daga dakin tattaunawar.

Wani abin ban mamaki shi ne, shugabannin Hamas sun bar wayoyinsu a cikin dakin tattaunawar, lamarin da ya bata leken asirin Isra’ila da cewa har yanzu shugabannin na nan a wurin da aka kai harin.

An kai harin ne ta hanyar amfani da makamai masu linzami 12 da jiragen yaki 15, kuma babban makasudinsa shi ne kashe manyan shugabannin Hamas Khalil al-Hayya, Zaher Jabarin, da Khaled Meshaal.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted