Shugaban kungiyar Ansar Allah, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ta kai kan kasar Yemen a ranar Laraba ba ta nuna wata nasara ba, sai dai yana nuna rashin bin dokokin kasa da kasa wajen ci gaba da aikata laifukan yaki.
A cikin jawabinsa na mako-mako a wannan Alhamis, yayin da yake magana kan sabbin abubuwan da suka faru dangane da hare-haren wuce gona da iri kan zirin Gaza da kuma abin da ya biyo bayan hakan, Sayyed al-Houthi ya bayyana cewa, kasar Yemen, a hukumance da kuma a matsayi na al’ummar kasar, tana a kan matsaya ta gaskiya, tana taka muhimmiyar rawa, kuma tana da cikakkiyar fahimtar abin da take aiwatarwa na sadaukarwa domin al’ummar Palastinu.
Ya kuma jaddada cewa, wuce gona da irin da Isra’ila ke yi da laifukan da take aikatawa ba za su raunana niyyar al’ummar kasar Yemen ba, a maimakon haka za su karfafa azama da kwarin gwiwarsu ne.
Sayyed al-Houthi ya yi kira da a gudanar da jerin gwano na miliyoyin mutane a wannan Juma’a a birnin Sana’a da kuma kowane dandali a fadin kasar.
Sayyed al-Houthi ya bayyana abubuwan da ke ci gaba da faruwa a Falasdinu, wadanda suke nuni aikata laifukan yaki a kullum rana da kuma kisan kiyashi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke aikatawa, a matsayin laifin yaki mafi muni a cikin wannan karni.