Araqchi: Hanya Daya Tilo Ta Kalubalantar Isra’ila Ita Ce Hadin Kai Tsakanin Kasashen Musulmi

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Hanya daya tilo ta kalubalantar ‘yan sahayoniyya ita ce ta hanyar hadin kai tsakanin kasashen musulmi Ministan

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Hanya daya tilo ta kalubalantar ‘yan sahayoniyya ita ce ta hanyar hadin kai tsakanin kasashen musulmi

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi, yayin da yake tsokaci kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai wa kasar Qatar, ya bayyana cewa, hanya daya tilo da za a bi wajen kalubalantar mummunar dabi’ar gwamnatin ‘yan sahayoniyya ita ce ta hanyar hada kai da hadin gwiwa tsakanin kasashen musulmi.

Araqchi ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a shafin sada zumunta na X a yammacin ranar Talata cewa: “Gwamnatin mamayar Isra’ila ta aikata wani mugun aiki kan Iran da ba za a iya tunani ba, a halin yanzu kuma ta kai hari ga al’ummar Qatar da kuma gwamnatin kasar Qatar.”

Ya kara da cewa: Iran na tsayawa tsayin daka da ‘yan uwanta na Qatar da Falasdinu, tana mai kakkausar suka ga wannan haramtaccen harin da aka kai a garuruwan da fararen hular gwamnatin Qatar ke amfani da su, wadanda ba su da wata barazana ga kowa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted