Kasashen Larabawa Da Na Duniya Sun Yi Allawadai Da Harin Isra’ila Doha

Kasashen larabawa da kungiyoyin kasa da kasa da wasu kasashen duniya sun yi tir da hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha babban birnin

Kasashen larabawa da kungiyoyin kasa da kasa da wasu kasashen duniya sun yi tir da hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha babban birnin Qatar a kokarinta na kashe shuwagabannin kungiyar Hamasa a yau Talata.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa babban sakataren MDD Antonio Gotterre ya yi tir da hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai birnin Doha na kasar Qatar ya kuma bayyana cewa hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Haka ma babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ahmad Gaith ya yi tir da hare-haren da HKI ta kai gine-gine a Doka.

Sannan kasashen Iran Saudia da Hadaddiyar daular Larabawa duk sun yi allawadai da hare-here. Gwamnatin kasar Turkiyya ta yi allawadai da kokarin kashe shuwagabannin kungiyar Hamas a doha.

Haka kuma shugaban kasar faransa Emmanuel Macron ya bayyana rashin amincewarsa da hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha na kasar Qatar da ko wani dalili ne.

Sai kuma shugaban kasar Lebanon Josept Aun ya yi tir da wadan nan hare-hare, tare da cewa suna barazana ga zaman lafiya a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted