Fira Ministan gwamnatin kasar Senegal ya nemi afuwar rashin amsa gayyatarsa ta farko a hukumance zuwa Faransa
Fira ministan Senegal Ousmane Sonko ya nemi afuwar rashin amsa gayyata a matsayin babban bako a zaman taron bugu na 11 na BPI France Generation Innovation Forum, wanda aka shirya gudanarwa ranar 23 ga watan Satumba a birnin Paris. Wannan zatab kasance ziyararsa ta farko zuwa Faransa tun bayan hawansa kan karagar mulki.
Fira Minista ya sanar a cikin wata sanarwa da aka buga a shafinta na yanar gizo da kuma dandalin X cewa: Sonko ba zai iya halartar gayyatar ba saboda “tsarin alkawurran da aka tsara,” tare da nuna cewa wani memba na gwamnatinsa zai wakilci Senegal a dandalin.
Wannan taron yana daya daga cikin fitattun tarurrukan tattalin arziki a Turai kuma a kowace shekara yana hada dubban masu zuba jari da ‘yan kasuwa.