Ma’aikatar harkokin wajen kasar Ghana ta sanar cewa ofishin jakadancinta dake birnin Tehran zai koma aiki a rana 16 ga watan satumnbar da muke ciki bayan rufeshi da aka yi na wucin gadi,
Sake bude ofishin jakadancin Ghana a birnin Tehran zai kara bude hanyoyi kyautata dangantakar Ilimi, kasuwanci, da musayar ala’adu da kuma yin aiki tare , adaidai lokacin da kawancen kasashen duniya ke canza sheka, wannan mataki ya nuna aniyar Ghana na karkatar da alakarta ta kasashen duniya.
An rufe ofishin jakadancin Ghana ne a ranar 16 ga watan yuni bayan yaki da ya barke tsakanin Iran da Isra’ila domin kare lafiyar ma’aikatanta a wannan lokacin .
Wannan matakin da kasar Ghana ta dauka na sake bude ofishin jakadancinta a iran ya nuna irin kokarin da kasashen Afrika ke yi na karfafa alaka da kasashen da ba na yamamcin turai ba, kuma zai kara saukaka hanyoyin yin hadin guiwar tattakin arziki da kuma yin aiki tare.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ya sanar da cewa bisa ci gaban da aka samu ta fuskacin tsaro a Iran jakadun kasashen duniya suna iya dawowa da ayyuka a ranar 16 ga watan satumbar shekarar da muke ciki.