Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Za Su Iya Komawa Zaman Tattaunawa Da Amurka A Kan Wasu Sharudda  

Ministan harkokin wajen Iran ya ce: A shirye Iran take ta gudanar da shawarwari da Amurka, amma kan sharudda Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi

Ministan harkokin wajen Iran ya ce: A shirye Iran take ta gudanar da shawarwari da Amurka, amma kan sharudda

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce; kasarsa a shirye take ta dawo da tattaunawar makamashin nukiliya da Amurka, amma tare da ba da tabbacin babu batun kai hari kan Iran. Ya bayyana cewa ba za a cimma abin da Amurka ke so ba ta hanyar kai harin soji kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, kuma a duk wata tattaunawa dole ne Amurka ta kare sharuddan da Iran ta gindaya mata domin samun ci gaba mai daure wa.

Araqchi wanda ya gana da Asharq Al-Awsat bayan halartar wani zama na musamman na ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi don tattaunawa kan goyon bayan Gaza da Falasdinu, bai nisanta yiwuwar bullar wata sabuwar arangama da haramtacciyar kasar Isra’ila ba, yana mai cewa: “Akwai yiwuwar komai ya faru, kuma Iran a shirye take ta kowane hali.”

Araqchi ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta shiga tattaunawa ta gaskiya da adalci dangane da shirinta na makamashin nukiliya, yana mai cewa a halin yanzu ana ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai uku da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa domin tantance sabon tsarin shawarwarin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted