Kasar Venezuala Ta Jinjinwa Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Kan Kyakkyawar Hadin Kai Da Ke Tsakanisu

Ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya bayyana jin dadinsa ga hadin kai da goyon bayan Iran ga kasarsa A wata tattaunawa ta wayar tarho da

Ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya bayyana jin dadinsa ga hadin kai da goyon bayan Iran ga kasarsa

A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Iran, ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya yabawa irin hadin kai da goyon bayan Iran ga ‘yancin kai, yana mai jaddada aniyar Iran na kare ta daga barazanar Amurka.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna da takwaransa na kasar Venezuela Ivan Gil Pinto ta wayar tarho game da alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaban da ake samu a yankin Caribbean.

A cikin wannan kiran, Ministan Harkokin Wajen Venezuela ya ba da rahoto kan abubuwan da ke faruwa a yankin Caribbean bayan karuwar barazanar Amurka da ikirarin haramtattun bukatu kan kasar Venezuela.

Da yake bayyana jin dadinsa ga irin hadin kai da goyon bayan Iran ga kasar Venezuela, ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya tabbatar da aniyar kasarsa, a matsayinta na al’umma da kuma gwamnati, na kare ‘yancin kai da ikon kasar, a kan muradun Amurka da barazanar da take yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted