Iran Ta Yi Kira Ga Kasashen Musulmi Su Yanke Hulda Da HKI A Taron OIC A Jedda

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi a jawabinda ya gabata a taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen musulmi ta OIC a birnin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi a jawabinda ya gabata a taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen musulmi ta OIC a birnin Kidda na kasar Saudia a yau Litinin, ya bukaci dukkan kasashen musulmi su yake hulda da HKI, su kuma dakatar da dukkan hulda da ita don tilasta mata kawo karshen kissan kiyashin da takewa falasdinawa a yankin.

Ministan ya bayyana cewa yakama kasashen su kawo karshen magana ba tare da daukar mataki ba. Yakamata su dauka matakai a kasa wadanda zasu iya hadawa sa yanke dukkan hulda da HK da kuma dakatar da huldar kasuwanci, da kuma kauracewa sayan dukkan kayakin da ake yi a HKI.

Ministan yan kara da cewa daukar matakin sharia, da daukar matakan takura mata a ko ta ina, zai taimaka wajen dakatar da kissan kiyashin na Gaza, da kuma shigar da binci isasshe ga falasdinawa a yankin.

Ya kuma yi maganar shirin HKI na cewa zata kafa Isra’ila babba, a fili ta bayyana haka ta kuma kara da cewa idan bamu dauki matakan da suka dace ba mai yuwa al-amara su kara lalacewa fiye da yadda yake a halin yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted