Harin Ukraine A Kan Bututun man Rasha Ya Saka Slovakia Da Hungary Cikin Tsoro

Harin da kasar Ukraine ta kai kan bututun man fetur na kasar Rasha ya sanya kasashen Hungary da Slovakia cikin zullumi na yiyuwar su daina

Harin da kasar Ukraine ta kai kan bututun man fetur na kasar Rasha ya sanya kasashen Hungary da Slovakia cikin zullumi na yiyuwar su daina samun man fetur.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a ranar Akhamis da ta gabata ce jiragen yakin kasar Ukraine wadanda ake sarrafasu daga nesa, wato ” Drones” suka kai hare-hare kann bututub man fetur na kasar Rasha dake Unecha na yankin  Bryansk wanda ya sa wutan mai yawa ya tashi a wurin. Ya kuma lalata ingin mai tura mai zuwa wasu kasashe a yankin.

Gwamnatin kasar Ukraine ta tabbatar da cewa ita ta kai harin, ta kuma kara da cewa kasar Rasha tana samun kudade masu yawa da man fetur da take sayarwa ta hanyar wannan bututun. Ana ganin harin zai tsaida kwarar mai daga wannan bututun har zuwa kwanaki biyar.

Labarin ya kara da cewa a halin yanzu dai kasashen Hungary da Slovakia ne kasashen turai da suka fi sayan man fetur na kasar Rasha. Bututun wandan ya tashi daga Rasha ya bi ta Belarus sannan ya tarsa ta Ukraine an gina shit un zamanin Tarayyar Soviet shi ne yake kai man fetur zuwa turai ta tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted