Sojojin Sudan sun yi nasarar fatattakar dakarun kai daukin gaggawa da magoya bayansu daga yammacin Kordofan
Sojojin Sudan sun yi nasarar fatattakar Dakarun kai daukin gaggawa a yankin Umm Qaud da ke yammacin Kordofan, inda suka janyo hasarar rayuka da kayan aiki ga ‘yan tawayen. A halin da ake ciki dai rundunar hadin guiwar ta musanta rahotannin da ke cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun karbe iko da filin tashi da saukar jiragen sama na El Fasher da ke arewacin Darfur.
Bayan da sojojin Sudan suka mamaye garuruwan Bara da Nahud da ke yammacin Sudan, bayan ficewar mafi yawan fararen hula, sojojin Sudan sun yi nasarar lalata daukacin ayarin motocin dakarun kai daukin gaggawa a yankin Umm Qaud da ke Arewacin Kordofan, inda suka lalata motoci 130 tare da kwace motoci 92 cikin sauki.