Yemen: Gangamin nuna goyon baya ga gwagwarmayar al’ummomin Falastinu da Lebanon

Miliyoyin mutane sun yi gangami a ranar Jumaa a birane daban-daban na kasar Yemen domin nuna cikakken goyon bayan ga gwawarmayar al’ummomin kasashen Lebanon da

Miliyoyin mutane sun yi gangami a ranar Jumaa a birane daban-daban na kasar Yemen domin nuna cikakken goyon bayan ga gwawarmayar al’ummomin kasashen Lebanon da Falastinu.

A cikin wata sanarwa da suka fitar, jerin masu gwanon sun ce muna goyon bayan gwarazan  gwagwarmayar Palastinawa da suke turmuza hancin makiya a  kasa a cikin ayyukansu masu ban mamaki da ba a taba ganin irinsu ba, suna mai tabbatar da matsayinsu na goyon bayan Gaza da kuma al’ummar Palastinu da ake zalunta.

Har ila yau, sun yi Allah wadai da sanarwar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta fitar na wani sabon mataki na wuce gona da iri kan birnin Gaza, da hakan ke samun goyon bayan Amurka, tare da yin Allah wadai da irin goyon bayan da wasu gwamnatocin kasashen Larabawa suke ba makiya domin cutar da al’ummar Falastinu, wanda kuma shi ne babban dalilin da yasa Haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kisan gillar da take yi a Gaza.

Baya ga haka kuma sun nuna goyon bayansu ga gwagwarmayar al’ummar Lebanon, tare da yin tir da duk wani yunkuri na kwance damarar kungiyar Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted