Kwamandan “IRGC” Ya Ce: Duk Wani Kuskuren Makiya Zai Fuskaci Martani Mai Gauni

Kwamandan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada cewa: Duk wani kuskure da makiya za su yi, za su gamu da amsa cikin gaggawa

Kwamandan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada cewa: Duk wani kuskure da makiya za su yi, za su gamu da amsa cikin gaggawa da yanke hukunci

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Mohammad Pakpour ya jaddada cewa: Iran za ta mayar da martani ga duk wani kuskuren da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta yi wajen tunkarar Iran ta hanyar mayar da martani mai tsauri, cikin gaggawa da kuma wurta cikin nadama.

Manjo Janar Mohammad Pakpour ya jaddada cewa: Gogewar yakin baya-bayan nan da Amurka da yahudawan sahayoniyya da suka kakaba wa Iran ya tabbatar da cewa, dabarun karfafa cikakken tsaro da kuma dogaro da karfin cikin gida zai hana makiya cimma munanan manufofinsu da kuma gargadin su kan su guji sabbin kasada.

Wannan dai ya zo ne a cikin sakon taya murna da babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Mohammad Pakpour ya aike zuwa ga ministan tsaro na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, dangane da zagayowar ranar masana’antun tsaron kasar.

Sakon ya ci gaba da cewa: Ko shakka babu babban abin alfahari da irin nasarorin da masana’antun tsaro suka samu a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, su ne sakamakon imani da dogaro da kai da himma da kuma namijin kokari na mutane masu aminci da juyin juya halin Musulunci wadanda a karkashin jagorancin babban kwamandan sojojin kasar (Allah ya kara fadada inuwarsa) sun tsara hanyar tabbatar da martabar kasar da kuma tabbatar da ‘yancin kai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted