Babban Kwamandan Sojojin Kasar Iran Ya Jaddada Shirin Iran Na Kalubalantar Makiya

Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya tabbatar da shirin sojojin kasar na mayar da martani ga duk wani harin wuce gona da iri Babban kwamandan

Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya tabbatar da shirin sojojin kasar na mayar da martani ga duk wani harin wuce gona da iri

Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya jaddada cewa: Jajirtattun sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun shirya tsaf a yau, kamar yadda suka yi a baya, domin mayar da martani mai tsauri ga duk wani mai wuce gona da iri.

Manjo Janar Hatami wanda ya aike da sakon taya murna ga ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh a daidai lokacin da ake gudanar da bikin zagayowar ranar masana’antun tsaro, ya jaddada a cikin sakonsa cewa, ci gaba cikin sauri da karfin tsarin tsaron Jamhuriyar Musulunci shi ne tasirin abin yabo da amanar tsare-tsare na dabaru na babban kwamandan kolin sojojin kasar Iran, Jagoran Juyin Juya Hali Imam Khamene’i (Allah ya kara masa aminci da tsaro) ga sojojin tsaron kasa da ma’aikatar tsaron kasar, musamman ma’aikatar tsaron kasar Iran da tallafawa dakarun sojojin tsaro.

Manjo Janar Hatami ya ci gaba da cewa: “Wadannan ci gaba na tsaro a cikin manhajoji da na’urori sun kai kololuwarsu a tsawon shekaru takwas na tsaro mai alfarma da kuma yakin kwanaki 12 da aka yi, wanda ya kai ga amincewar duniya yadda kasar Iran ta dogara da karfin al’ummar kasar da kuma karfinta na cikin gida da kere -keren ta na cikin gida.”

Manjo Janar Hatami ya jaddada cewa: Imani da masana kimiyyar cikin gida da kuma dogaro da nau’o’in kayayyakin kariya na cikin gida a daidai lokacin da ake kakaba wa Iran takunkumi na rashin adalci, ya tabbatar da cewa Iran ba za ta jira izinin wani bako ba don samar da kuma amfani da bukatun tsaronta wajen kare tsaron kasa, ‘yancin kai, da tsarin Jamhuriyar Musulunci mai tsarki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted