Sojojin Kasar Lebanon sun fara karban makamai daga hannun falasdinawa a sansaninsu dake Burjul Barajina da ke kudancin birnin Beirut. Wannan a shekarin shirin sabuwar gwamnatin kasar Lebanin na kwace dukkan makaman daga hannun kungiyoyiu daban-daban a kasar daga ciki har da kungiyar Hizbullah a matsayin taimakonsu ga HKI na mamaye kasar Lebanon bayan haka.
Shafin yanar Gizo na Labarai Arab News na kasar saudiya ta bayyana cewa wannan shirin na karban makamai daga kungiyoyi a kasar ta Lebanon ya hada da kungiyar Hizbullah na kasar wacce ta dauki shekaru da dama tana kare kasar daga .
A ranar 5 ga watan Auguistan da ya gabata ne gwamnatin kasar Lebanon karkashin firai minister Nawaf Slam ta tsaida shawarar kwace makaman hizbullah.