Kwamitin kungiyoyin wagwarmaya a Iraki ya sake jaddada shirinsa na tunkarar ta’addancin Amurkawa, tare da jaddada cewa makamansu za su ci gaba da kasacewa a cikin shiri domin kare Iraki da al’ummarta tare da hadin gwiwa da sauran bangarorin tsaro da suka hada da dakarun sa kai na Hashd Al Shaabi, ko kuma Popular Mobilization Forces (PMF).
Kwamitin ya jaddada cewa dole ne a kiyaye martabar masu kare kasar Iraki, sannan kuma kada a keta alfarmar sansanonin da suke da su, tare da yin la’akari da sansanin Saqr na PMF, cibiyar da ta dade tana samar da mayaka wadanda suka tsaya tsayin daka a matsayin masu kula da kasa da tsarin siyasarta na yaki da makirce-makircen kasashen waje da ta’addanci.
A cikin sanarwar da kwamitin ya fitar, ya bayyana cewa bakaken manufofin Washington na kiyayya ga al’ummomin yankin ba za su taba canzawa ba.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, a yayin da sojojin Amurka ke mayar da kansu a yankunan da suke ganin sun fi tsaro da kuma rage yawan sojojin da ke wasu sansanonin, a lokaci guda kuma sun kara zafafa ayyukan keta hurumin kasar Irakin ta hanyar kara sanya ido a sararin samaniya wanda Wadannan ayyuka na a matsayin cin zarafi da keta alfamar al’ummar Iraki.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Kata’ib Hezbollah da sauran kungiyoyin gwagwarmaya a Iraki suka yi gargadin cewa duk wani yunkuri na Washington na shiga a rikicin da ke faruwa tsakanin “Isra’ila” da Iran, zai bude kofar sake kai hare-hare kan sojojin Amurka a Iraki da ma yankin baki daya.