Ministan harkokin wajen kasar Jordan ya bayyana cewa yaka a kan Gaza wanda ya kashe dubban falasdinawa, da kuma kara fadada shi a halin yanzu ta gwamce yanking aba daya daga kungiyar Hamas, mai yuwa da fitar da Falasdinawa da karfi daga gidajensu zuwa wasu yankuna, ya wargaza duk fatan da ake da shin a samun zaman lafiya mai dorewa a gabas ta Tsakiya.
Shafin yanar gizo na labarai ‘arabnes’ na kasar Saudiya ya nakalto Ayman Assafadi yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da tokwarans na kasar Rasha Sergei Lavlov a birnin Mosco. Ya kuma bayyana haka ne bayan da ministan harkokin yakin HKI Isra’il Katz ya bayyana cewa suna shirin kwace Gaza gaba daya , wanda birnin ne inda dubban daruruwan falasdinwa suke rayuwa.
Assafadi ya kara da cewa, HKI tana kara yin wasu ayyuka wadanda suke kara nisantar samar da kasashe biyu a kan kasar Falasdinu da ta mamaye.
Majiyar asbitocin Gaza sun bayyana cewa, ya zuwa yanzun dai sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa akalla dubu 62,000 kuma