Gwamnatin Donald Trump ta kakaba wa wasu jami’ai hudu na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya takunkumi (ICC) takunkumi, lamarin da ya kara ta’azzara takun saka da Washington ke yi da kotun kan shari’o’in da suka shafi Amurka da gwamnatin Haramtacciyar Isra’ila.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Laraba, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana kotun ta ICC a matsayin barazana ta tsaron kasa ga Amurka da kawayenta.
Takunkumin dai ya shafi alkalai Nicolas Yann Guillou na Faransa da Kimberly Prost na Canada, tare da masu gabatar da kara Nazhat Shameem Khan na Fiji, da Mame Mandiaye Niang na Senegal. Duk wadannan jami’ai suna da alaka da lamuran shari’a a wannan kotu da suka shafi gwamnatocin Isra’ila da Amurka.
Ya ce “Amurka ta fito karara kuma ta tsaya tsayin daka wajen adawa da siyasar ICC, kana bin da ya kira cin zarafi, rashin mutunta ‘yancin kai, da kuma tozarta shari’a,” in ji Rubio.
Takunkumin dai ya dakatar da duk wasu kadarorin Amurka da jami’an hudu ke rike da su, tare da katse su daga tsarin hada-hadar kudi na Amurka. Matakin na zuwa ne kasa da watanni uku bayan da Washington ta kakabawa wasu alkalan kotun ta ICC takunkumi, wanda ke zama zagaye na biyu na daukar irin wannan matakin a kan jami’an kotun duk a cikin wannan shekara.
Kotun ta ICC ta bayar da sammaci a watan Nuwamban da ya gabata domin kame Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, da tsohon ministan tsaro Yoav Gallant, da shugaban bangaren soji na Hamas Ibrahim al-Masri (Mohammad Deif) bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Gaza.