An fara yakin neman zabe a kasar Uganda don zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a shekara ta 2026 mai zuwa., inda jam’iyya mai mulki da kuma jamiyyun adawa duk sun fara yakin neman zabe.
A ranar 19 ga watan Augustan da muke ciki ne, jam’iyyar shugaban kasa ta ‘National Resistance Movement (NRM), ta gabatar da shirin yakin neman zaben shugaba ma ice Uwere Musevin na zaman watan jeneru mai zuwa.
Manya manyan yan siyasar jam’iyyar NRM kamar Al-Hajj Moses Kigongo da kuma Richard Todwong sune suka bude yakin neman zabe na shugaban kasa.. Hakama sauran Jam’iyyun adawa sanansu kamar the National Unity Platform (NUP), the Democratic Party (DP) duk sun kaddamar da kamfai na neman kujerar shugabancin kasar.
Sannan hukumar zabe ta bayyana cewa mutane kimani 177 suka bayyana anniyarsu ta shiga takarar shugabancin kasar. Amma zata tantance a nan gaba don fidda yan kadan wadanda zasu tsaya zaben tare da shugaban kasa mai ci. Mesevene dai yana shugabancin kasar Uganda sun shekara 1986, ya yi zagaye 6 na shugabancin kasar sannan ya na shirya shiga zagaye na 7 a zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a ranar 12 ga watan Jeneru mai zuwa.