Firayim Ministan Sudan ya  kirayi MDD da a kawo karshen killace El Fasher da RFS ke yi

Firaministan Sudan Kamil Idriss ya aike da sakon gaggawa ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bukaci kwamitin sulhu da Majalisar Dinkin Duniya da

Firaministan Sudan Kamil Idriss ya aike da sakon gaggawa ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bukaci kwamitin sulhu da Majalisar Dinkin Duniya da su dauki kwararan matakai na ganin an kawo karshen killace El Fasher da dakarun RSF ke yi, tare da bude hanyoyin jin kai don kai agaji ga al’umma, da kuma hana yin amfani da yunwa domin azabtar da fararen hula.

Kamfanin dillancin labaran Sudan ya nakalto Idriss na cewa a cikin wasikar tasa,  “An yi wa birnin El Fasher kawanya, kuma dubban daruruwan fararen hula ne suka makale a ciki, yayin da iyalai ke fama da yunwa, kana yara ke mutuwa a gaban iyayensu saboda karancin abinci da kuma kayayyakin bukatar rayuwa da magunguna.”

Ya jaddada cewa, abin da ke faruwa a El Fasher babbar jarabawa ce ga Majalisar Dinkin Duniya, yana mai cewa dokokin kasa da kasa sun haramta amfani da yunwa a matsayin makamin yaki.

Idriss ya ci gaba da cewa, “Hakkin rayuwa, abinci, da kuma kula da lafiya, haƙƙin ɗan adam ne na asasi. Amma duk da haka, ana tauye waɗannan haƙƙoƙin a El Fasher a kowace sa’a.” Firaministan Sudan ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da su dauki matakin gaggawa, domin kawo karshen killace yankin tare da bude hanyoyin jin kai.

Ya kara da cewa “Al’ummar El Fasher ba za su iya jira a ci gaba da tattaunawa ko kuma yanke shawarwarin da za a yanke ba,” domin “rayuwar su ta dogara ne da matakin gaggawa da bangarori na kasa da kasa za su dauka domin ceton rayuwarsu.”

Idris ya kammala da cewa, “Tarihi zai rubuta ko Majalisar Dinkin Duniya ta zabi yin shiru tare da barin wani gari baki daya ya halaka, ko kuma za ta yi tsaya tsayin daka don kare wadanda ba su ji ba su gani ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted