Larijani: Ba Zasu Amince Da Yin Kutse A Alakar Da Ke Tsakanin Iran Da Iraki Ba

Babban sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba zasu yarda wasu kasashe su shiga tsakanin Iran da Iraki ba Yayin da yake

Babban sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba zasu yarda wasu kasashe su shiga tsakanin Iran da Iraki ba

Yayin da yake magana game da rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro tsakanin Iran da Iraki, babban sakataren majalisar koli na tsaron kasar Iran Ali Larijani  ya yi nuni da cewa: Bai kamata a bar kasashe uku su tsoma baki cikin fahimtar juna da tsaron da ke tsakanin kasashen biyu ba, ko kuma su yi amfani da yankin wata kasa a kan wata kasa.

Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya tattauna da shirin “Tehran-Tel Aviv” da aka watsa a gidan radiyo da talabijin na kasar Iran kan ziyararsa ta farko a wannan matsayi a kasashen Iraki da Lebanon, da kuma game da halin da yankin yake ciki, yana mai cewa: Babu shakka batutuwan yankin suna daga cikin muhimman batutuwan da suka shafi moriyar kasa da tsaron kasar Iran, kuma a hakikanin gaskiya al’amurran da suka shafi tsaron yankin sun ginu ne bisa dabarun da suka dace na tsarin Jamhuriyar Musulunci.

Larijani ya kara da cewa: Akwai wasu muhimman layuka ko hangen nesa guda biyu dangane da batun tsaron kasa, yana mai cewa: Wata ka’ida ta ce Amurka da Isra’ila suna bayyanawa a fili a yau cewa suna son zaman lafiya da karfin tsiya, wanda ke nufin ko dai a mika musu wuya ko kuma su kaddamar da yaki. Sakamakon wannan ra’ayi na neman dagula lamura a yankin da ake gani a aikace a kasar Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted