Ma’aikatar Leken Asirin JMI Ta Ce Ta Gano Shirin Kashe Manyan Mutane 35 a kasar

Ma’aikatar leken asiri na JMI ta bada sanarwan cewa ta gano shirin makiya na kashe manya-manyan Jami’an gwamnati har 35 a kasar kafin yakin da

Ma’aikatar leken asiri na JMI ta bada sanarwan cewa ta gano shirin makiya na kashe manya-manyan Jami’an gwamnati har 35 a kasar kafin yakin da suka dorawa kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar na fadar haka, ta kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 sun yi kokarin kashe many-manyan Jami’an gwamnati har 35 a cikin yakin. Da kuma wasu 13 watanni kafin yakin, amma saboda matakan da ma’aikatar ta dauka hakan bai faru ba.

Labarin ya kara da cewa, hukumar a tsaye take kan makirce-makircen makiya, sannan kuma tana daukar matakan da suka dace don hana  kutsawar su a cikin kasar da kuma cutar da shuwagabanni da kuma mtanen gari.

A wani bangare kuma hukumar ta bayyana cewa tana ayyukan leken asiri kan HKI da kuma shirye-shiyenta nag aba. Tana samun ma’aikata a cikin sojoji da jami’an tsaro na HKI. Sannan ta kara da cewa ma’aikatansu kadanne yahudawan suka kama.

Majiyar ta kara da cewa ta sami bayanan sirri kan shirye-shrye masu muhimmanci na HKI daga ciki har da bayani dangane da shirinta na makaman Nukliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted