Iran Da Kasashen Turai uku Zasu Farfado Da Tattaunawa Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya A Istambul

Ma’aikatar harkokin wajenn kasar Iran ta bayyana cewa, kasar Iran zata halarci taro don tattauna shirin makamashin nukliya da kasar Iran da kuma dauke mata

Ma’aikatar harkokin wajenn kasar Iran ta bayyana cewa, kasar Iran zata halarci taro don tattauna shirin makamashin nukliya da kasar Iran da kuma dauke mata takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata a ranar Jumma’a  mai zuwa a kuma birnin Estambul na kasar Turkiya..

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran yana fadar haka a jiya Litinin a lokacinda yake ganawa da kafafen yada labarai a ranakun litinin kamar yadda ya saba.

Labarin ya kara da cewa jami’an kasashen 4 da zasu halarci taron Istambul masu matakin mataimakan ministocin harkokin waje ne.

Labarin ya kara da cewa tattaunawa da kasashen turai 3 dangan da shirin nukliyar kasar Iran da kuma daukewa kasar takunkuman da suka dora mata, baya daga cikin tattaunawa ba kai tsaye ban a tsakanin Iran da Amurka.  A tattaunawa tsakanin Iran da Amurka dai amurkawan sun ki su gayyaci turawan musamman Jamau da faransa da kuam Ingila wadanda suke cikin yarjeniyar GCPOA ta shekara ta 2015.

Labarin ya kara da cewa Iran ta tattaunawa da wadannan kasashen Turai ukku E3 a kebe har sau 4, a NewYok da Geneva da har sau biyu da kuma Istambul a ranar jumma mai zuwa. A wannan karon dai kasashen 3 ne suka bukaci a gudanar da taron na Istambul.

“Majid Takht-Ravanchi da Kazem Gharibabadi, mataimakan ministocin harkokin wajen kasar ne zasu wakilci kasar Iran a taron.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted