Shugaban Darikar Katolika ta Mabiya Addinin Kirista Fafaroma ya yi kira da a kawo karshen ‘zaluncin yaki’ a zirin Gaza
Fafaroma Leo na 14 ya yi kira a jiya Lahadi da a kawo karshen zaluncin yakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, yana mai bayyana bakin cikinsa kan harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a baya-bayan nan kan cocin Katolika daya tilo a yankin. Ya kuma jaddada cewa kai hare-hare a wuraren ibada babban cin zarafi ne ga mutuntaka da addini.
Fafaroma ya yi kira ga al’ummomin kasa da kasa, inda ya bukace su da su kiyaye dokokin jin kai, da mutunta wajibcin kare fararen hula, da hana azabtar da jama’a, da nisantar yin amfani da karfi ba gaira ba dalili, da kuma tilasta wa al’umma gudun hijira.
Tun da farko, yayin gabatar da jawabai na mako-mako a dandalin St. Peter, Fafaroma ya yi kira da a kawo karshen hare-haren da ake kai wa Gaza, yana mai cewa, “A zirin Gaza kukan uwa da uba, da suke rungume da gawar ‘ya’yansu da aka kashe, suka tashi sama.”
Wadannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke kara matsin lamba na dakatar da yakin da ake yi a yankin, a daidai lokacin da ake samun ci gaba da tabarbarewar al’amuran jin kai a Gaza.