‘Yan gwagwarmaya sun sanar da kai hari kan tankokin yakin sojojin mamayar Isra’ila guda uku a yankin Shuja’iyya

Dakarun Sarayal- Quds bangaren sojin kungiyar Jihadul- Islami, sun sanar a yammacin jiya Lahadi cewa: Mayakansu tare da hadin gwiwar dakarun Izzaddeen al-Qassam, bangaren sojin

Dakarun Sarayal- Quds bangaren sojin kungiyar Jihadul- Islami, sun sanar a yammacin jiya Lahadi cewa: Mayakansu tare da hadin gwiwar dakarun Izzaddeen al-Qassam, bangaren sojin Kungiyar Hamas sun yi nasarar kai hari kan tankokin yakin sojojin mamayar Isra’ila guda uku a unguwar Shuja’iyya da ke gabashin birnin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Today cewa: ‘yan gwagwarmayar sun bayyana a cikin wani sako da suka fitar a shafinsu na Telegram cewa: “Bayan sun dawo daga fagen daga… mayakansu sun tabbatar da cewa; Gamayyar ‘yan gwagwarmaya sun kai hari kan tankunan yaki na Merkava na sojojin mamayar Isra’ila guda uku, a wani harin kwantan bauna da suka kai da bama-bamai da makami mai linzami kan tankokin yakin a Unguwar Shuja’iyya a gabashin birnin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted