Tsohon Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Isra’ila Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiyar Duniya

Tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Zaman lafiya yana fuskantar barazana ne kawai sakamakon wanzuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya Tsohon ministan harkokin wajen

Tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Zaman lafiya yana fuskantar barazana ne kawai sakamakon wanzuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya

Tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewa yaki, ta’addanci, zagon kasa, da kuma muggan laifuka .. na nuni da cewa “barazana ce da ke akwai” wanda yake zuwa daga ‘yan sahayoniyya kawai.

Tsohon ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Jawad Zarif ya rubuta a shafinsa na X cewa: “Bari mu yi dubi: harin da aka kai Siriya, harin da aka kai wa Lebanon, da yakin Iran, da kisan kiyashi a Gaza, da harin bama-bamai kan Yemen, da hamayya ga tsarin aiki na hadin gwiwa, da kin amincewa da yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, da yarjejeniyar hana samar da makamai masu guba, da sauran tsare-tsare na hana samar da makamai masu hadari da makaman kare dangi, da makaman nukiliya har da tsare-tsaren Amurka da Tarayyar Turai duk gwamnatin ‘yan sahayoniyya sun saba musu.”

Don haka yaki, ta’addanci, zagon kasa, muggan laifuka … duk suna nuni da cewa sune barazanar daya tilo ake fuskanta wadanda suke tattare a haramtacciyar kasar Isra’ila da bata kaunar zaman lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted