Rahotonni suna bayyana cewa; Mutane sama da 360 ne a ka kashe a birnin Suweida na kasar Siriya bisa ga kididdigar farko
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta kasar Siriya, ta sanya ido kan farkon janyewar dakarun ma’aikatar tsaron kasar Siriya daga lardin As-Suweida.
Janyewar dai na zuwa ne bayan shafe kusan sa’o’i 90 ana gwabza kazamin fada a cikin birnin da kewaye, wanda ya hada da yanke hukuncin kisa da kuma cin zarafi da wadannan sojoji suka yi kan fararen hula da mayakan yankin.
A wani kididdigar farko da kungiyar kare hakkin bil’adama ta yi ta tattara bayanan mutuwar mutane 360, a daidai lokacin da aka samu rahoton mutuwar mutane da dama a tsakanin fararen hula, mayakan Druze, da dakarun gwamnati.
Adadin wadanda suka mutu tun safiyar Lahadi, 13 ga watan Yuli, sakamakon fadace-fadacen da aka yi, da kisa a fili, da kuma harin bama-bamai na sojojin mamayar Isra’ila, ya kai mutane 360,
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Syria ta yi gargadi game da sake faruwar irin wannan ta’asa tare da yin kira ga kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin bil’adama da su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu na kare fararen hula tare da tabbatar da hukunta wadanda suka aikata laifukan a lokacin ayyukan soji a Sweida.