Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta sanar da cewa: Mutane biyu ne suka yi shahada wasu uku kuma suka jikkata a hare-hare biyu da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a kudancin kasar Lebanon
Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da shahadar wasu ‘yan kasar biyu tare da jikkata wasu uku sakamakon hare-hare ta sama da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a kudancin kasar.
Ma’aikatar ta bayyana, ta hanyar Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Lafiyar Jama’a, cewa: Daya daga cikin hare-haren ta sama ya auka wa wata motar farar hula a kan babbar hanyar Toul-Kufour a gundumar Nabatieh, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu biyu na daban.
A wani hari na biyu da makiya suka kai ta sama ta hanyar amfani da jirgin sama mara matuki kan wata babbar mota a garin Naqoura da ke kan iyaka, wani dan kasar Lebanon ya mutu nan take.