Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai Za Ta Bunkasa Nan Kusa Kadan

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Nan ba da jimawa ba kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai za ta wuce yankinta Ministan harkokin wajen kasar

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Nan ba da jimawa ba kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai za ta wuce yankinta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Sannu a hankali kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai tana kara fadada kasancewarta a duniya, kuma nan ba da dadewa ba za ta fadada karfinta fiye da yankinta.

Araqchi ya ce da isarsa kasar China a safiyar yau Talata: “Ziyararsa a kasar China ita ce halartar taron ministocin harkokin wajen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 25, wanda za a yi gobe Laraba a birnin Tianjin karkashin inuwar kasar China.” Ya kara da cewa: “Kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai sannu a hankali tana kara bude kofa ga kasashen duniya, ma’ana nan ba da dadewa ba za ta zarce a shiyya, kuma ajandarta ta kunshi batutuwa daban-daban, wadanda suka shafi tattalin arziki, siyasa, ko tsaro.”

Araghchi ya ci gaba da cewa: “A wannan taro, za a amince da dabarun raya kungiyar da kasashe mambobinta a fannonin makamashi, cinikayya, da sauran fannoni. Har ila yau, za a gudanar da tattaunawa kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa a halin yanzu.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted