Mutane da dama suka ji raunin sannan an lalata gidajen mutane da kuma wasu na gwamnati a lardunan Lipetsk da Voronezh na kasar Rashi a daren jiya inji gwamnonin wadannan larduna na kasar Rasha.
Shafin yanar gizo na labarai ‘arabnews’ na kasar Saudiya ya kara da cewa majiyoyin wadan nan larduna sun bayyana cewa garkuwan makamai masu linzami na kasar Rasha sun sami nasarar kakkabo jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa har 55 a daren Talata 15 ga watan Yulin shekara ta 2025.
Gwamnan jihar Voronezh Alexander Gusev ya rubuta a shafinsa na Telegram kan cewa garkuwan tsaron sararin samaniyar kasar Rasha sun sami nasarar kakkabo jiragen Drons har 12 a lardinsa wanda yake makobtaka da kasar ta Ukraine, sannan ya tabbatar da cewa akwai wadanda suka ji rauni amma babu mutuwa ko guda. Ya kara da cewa mutane da dama sun ji kananan raunuka saboda tarwatsewar jiragen da aka tarwatsa. Ya ce hakam ma gidajen mutane da kuma wasu gine ginen gwamnatin sun lalace saboda tarwatsewar jiragen Drones din. A birnin Yelets na lardin Lipetsk kuma , gwamnan lardin Igor Artamonov ya bayyana cewa wani jirgin ya fadi kusa da unguwar kamfanoni .
Daga karshe garkuwar makamai masu linzami na kasar ta rasha sun kakkabo jirage yakin har 55 a larduna 5 da suke kusa da kasar Ukraine.