Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Iran ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin kuskuren kai hari kan Iran, lallai zasu fuskanci mayar da martani da karfi
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdurrahim Mousawi ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin kuskure to za su fuskanci martani mai radadi da karfi da zai wurga su cikin nadama.
A yayin ganawarsa da gungun mayakan sojojin sama, Manjo Janar Mousawi ya mika sakon jinjina ga shahidai madaukaka da karfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran musamman shahidi Major Janar Hajj-zadeh. Ya yaba da rawar da yake takawa wajen ciyar da shirye-shirye dabarun rundunar Sojin sama da inganta karfin makamai masu linzami da jiragen sama na kasar, ya kuma yi la’akari da kokarinsa a matsayin mai karfi da zaburarwa ga al’ummomi masu zuwa masu kishin kare kasarsu.
Mousawi ya bayyana sojojin sararin samaniyar dakarun juyin juya halin Musulunci a matsayin wani karfi da ke haifar da alfahari da mutuntawa, yana mai cewa, “Bayyana wannan karfin da sojojin sararin samaniya suka yi a lokacin yakin kwanaki 12 da aka kafa ya zarce duk wani abu da aka cimma ya zuwa yanzu, kuma ya fi muhimmanci fiye da manyan ayyukan da aka yi a lokacin tsaro mai alfarma.”
Mousawi ya kara da cewa ba a taba fuskantar irin wannan barazana da wanzuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma cikakken yankin kasar Iran ba, yana mai cewa: To amma wannan takwabi mai yankan ra’ayi na sojojin sararin samaniya cikin yardar Allah ne suka yi nasarar buge wuyan makiya tare da yanke hannayensu.