EU Ta Ce Zata Maida Martani Kan Amurka Da Kudaden Fito Na Euro Biliyon 21 Tare Da Yiyuwan Kari

Kungiyar tarayyar Turai UE ta bada sanarwan cewa ta shirya tsab don amidawa gwamnatin Amurka martani na kudaden fito mai yawan Euro billion 21, tare

Kungiyar tarayyar Turai UE ta bada sanarwan cewa ta shirya tsab don amidawa gwamnatin Amurka martani na kudaden fito mai yawan Euro billion 21, tare da yiyuwan kara shi, a matsayin martani ga kasar ta Amurka na karin kudaden fito na kasha 30% kan kasashen kungiyar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar tarayyar Turau daga Brussels na cewa, kodaden fiton da Amurka ta daurawa kasashen kungiyar yana dai dai da kashe harkar kasuwanci ne da ita.

Labarin ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani yana yana fadar haka ga wata jaridar kasar, kan cewa wannan maida martanin zai fara aiki ne matukar tattaunwa tsakanin bangarorin biyu, wanda yake gudana a halin yanzu  ya kasa warware matsalar.  

A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donaltrump ya bayyana cewa zai karawa kasashen Mexico da kuma kasashen turai karin kudin fito har zuwa kahi 30% wanda zai fara a ranar 1 da watan Augusta mai kamawa idan sun kasa fahintar juna a tattaunawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted