Ministan Yakin Gwamnatin Mamayar Isra’ila Yana Alfahari Da Rusa Zirin Gaza Na Falasdinu!

Ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana alfahari da rusa Gaza da tarwatsa mazauna yankin! Isra’ila Katz, ministan yakin gwamnatin mamayar Isra’ila, ya wallafa wani

Ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana alfahari da rusa Gaza da tarwatsa mazauna yankin!

Isra’ila Katz, ministan yakin gwamnatin mamayar Isra’ila, ya wallafa wani hoto da ya nuna yadda aka lalata garin Beit Hanoun a arewacin zirin Gaza, yana mai alfahari da yadda aka rusa gine-ginen garin”.

Kuma ta hanyar dandalin “X”, Kats yayi sharhi game da hoton, yana cewa: “Bayan Rafah da Beit Hanoun.. babu mafaka ga ‘yan ta’adda.

Hoton da aka dauka ta sama yana nuni da dimbin baraguzan gine-gine da kango da kuma irin barnar da aka yi wa daukacin garin da ke daura da layin da aka shimfida da tarwatsewar kango da ragowar gine-ginen da suka ruguje a hoton inda ke nuni irin girman bala’in da ya afku a yankin.

Beit Hanoun shi ne yanki na farko da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka mamaye a farkon harin na kasa a Gaza a ranar 28 ga watan Oktoban shekara ta 2023, a ci gaba da yakin kisan kiyashi bayan barna da Falasdinawan sama da dubu 195 suka yi shahada da kuma jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted