Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; An Mika Batun Hakin Gwiwa Tsakanin Iran Da Hukumar IAEA Ga Kwamitin Kolin Tsaron Kasa

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: An mika fayil ɗin haɗin gwiwa tare da Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: An mika fayil ɗin haɗin gwiwa tare da Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ga kwamitin koli na tsaron ƙasa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana a wata ganawa da jakadun kasashen waje da na kasa da kasa cewa: Iran bangare ce a yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta “NPT” kuma tana yin aiki da tanade-tanaden da aka yi mata, amma idan aka yi la’akari da sabbin yanayi da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, hadin gwiwarta da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA za ta dauki wani sabon salo.

Yayin da yake ishara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da tsayawa tsayin daka kan yarjejeniyar tsaron da aka kulla tsakaninta da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, Araqchi ya ce: Hadin gwiwar Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya bai tsaya ba, amma idan aka yi la’akari da sabbin yanayi da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, wannan hadin gwiwa zai dauki wani sabon salo. Wannan gaba ɗaya al’ada ce kuma ana tsammanin hakan.

Shugaban jami’an diflomasiyyar na Iran ya ci gaba da cewa: Kamar yadda dokar majalisar shawarar Musulunci ta tanada, daga yanzu, kwamitin koli na tsaron kasar zai gudanar da dukkanin hadin gwiwar da Iran za ta yi da hukumar ne kawai, kuma wannan majalisar za ta yi nazari tare da yanke hukunci kan kowane lamari da hukumar ta bukaci ci gaba da sanya ido a Iran. Za a gudanar da waɗannan bita tare da cikakken la’akari da lura cikin aminci da tsaro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted