Hukumar Makamashin Nukliya Ta Kasar Iran Ta Tabbatar da Cewa HKI Ta kai Hari Kan Cibiyar Natanz

Hukumar makamashin nukliya ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa jiragen yakin HKI sun kai hare hare kan cibiyar tace makamashin uranium ta kasar dake

Hukumar makamashin nukliya ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa jiragen yakin HKI sun kai hare hare kan cibiyar tace makamashin uranium ta kasar dake Natanz kuma ya lalata wani bangare na cibiyar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hare haren da HKI ta kawo nan Iran a safiyar yau Jumma’a ya shafi cibiyar tashe uranium ta Natansa amma ba wanda ya rasa rainsa ko ya jikata a can.

Cibiyar wacce ake kiranta Shahid Ahmadi Roshan ya lalace saboda hare  hare haren na HKI amma ba wadanda suka shafi kayakin aikin tashe uranium ba.

Labarin ya kara da cewa jiragen yakin HKI sun kai hare hare kan larduna da dama daga ciki har da Tehran, Tabriz, Kermanshah, Khorramabad, Boroujerd da Esfahan duk a tsakiyar kasar.

Wasu labaran wadanda tashar talabijin ta Almayadeen ta nakalto daga wata majiya a nan Tehrann tace mai yuwa a dazu dazun nan yahudawan sun kai hare hare a lardin Azerbainan ta gabasa. Amma babu karin bayani har yanzun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted