Ma’aikatar lafiyar kasar Sudan ta bayyana cewa: Ana ci gaba da daukan matakan ganin an shawo kan ci gaba da yaduwar masifar kwalara a kasar
Gidan talabijin na Al-Alam ya watsa rahoton cewa: A halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya a birnin Khartoum fadar mulkin kasar bayan bullar cutar kwalara yana ta kokarin ya shawo kan matsalar tare da killace mutanen da suka kamu da cutar a wurare na musamman a babban birnin kasar Khartoum, rahotonni sun bayyana cewa: Cutar ta bazu cikin sauri a birnin. Sannan ma’aikatar lafiya ta Sudan da kungiyoyi da dama suna ci gaba da kokarin shawo kan cutar don kada ta zama annoba wadda za ta yadu zuwa jihohi da dama.
Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya yi nuni da cewa: Akwai kuma jahohi da dama a yankin Darfur, wadanda wasu daga cikinsu suka kamu da cutar kwalara, inda ya ce daya daga cikin abubuwan da ke kawo wannan cuta shi ne yanayin da ake fama da shi a yankin Al-Salha, inda aka shafe fiye da wata guda ana gwabza fada tsakanin sojojin Sudan da ‘yan tawayen kasar na dakarun kai daukin gaggawa, inda gawarwakin mutane suke kwance a gefen hanya, kuma sun kwashe sama da wata guda, babu wani yunkurin kwashe su, don haka suke wari tare da gurbata yanayi, wasu gawarwakin kuma aka kai su cikin teku. Duk wannan na daya daga cikin dalilan da suka haifar da yaduwar wannan cuta, amma ta dan ja da baya, a cewar ministan lafiya na tarayya, wanda ya zo musamman Khartoum domin fayyace lamarin.