Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ba Ta Da Alkiblar Siyasa

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani yanki na siyasa mai zaman kansa Shugaban Majalisar Shawarar

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani yanki na siyasa mai zaman kansa

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba su da wata kafa ta siyasa mai cin gashin kanta, a maimakon haka dole ne a fahimci matsayinsu geopolitical bisa tsarin mulkin Amurka.

A jawabin da ya gabatar a wajen rufe taron tattaunawa na Tehran a jiya litinin, Qalibaf ya kara da cewa: A fagen siyasar kasa, siyasa ba ita ce kullin nauyi ba, a maimakon haka, labarin kasa shi ne ginshikin da siyasa ta ginu a kansa a matsayin wani mataki mai girma.

Ya bayyana cewa: Idan ana magana game da ababen more rayuwa da labarin ƙasa ke wakilta a zahiri, ana nufin nazarin abubuwa uku: Wuri, mutane da lokaci. Wato fahimtar nazarin al’amuran ɗan adam a lokuta daban-daban yana samuwa ne ta hanyar nazarin fifikon wuri. Don haka, a cikin binciken a fagen siyasa, za a dogara da wuri a matsayin tushen abubuwan more rayuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted