Iran: Aiwatarda Yarjeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Armenia Da Arzerbaijan Zai Tabbatar Da Zaman Lafiya A Tsakanin Kasashen Biyu

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa  aiwatar da yarjeniyar zaman zaman lafiya wadanda aka cimma tsakanin kasashen Armenia da kuma Azerbaijan

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa  aiwatar da yarjeniyar zaman zaman lafiya wadanda aka cimma tsakanin kasashen Armenia da kuma Azerbaijan da gaggawa zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin kasashen biyu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto Aragchi yana fadar haka a lokacin ganawarsa da sakataren majalisar koli ta tsaron kasar  Armenia, Armen Grigoryan  wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran a yau Asabar.

Ministan ya kara da cewa JMI zata tabbatar da cewa an aiwatar da sulhu tsakanin kasashen biyu da gaggawa saboda tana dasawa da kasashen biyu makobta gareta.

A cikin watan Maris da ya gabata ne kasashen Armenia da Arzerbaijan suka amince a rubuta yarjeniyar sulhu a tsakaninsu a tsakaninsu don kawo karshen rikici a tsakaninsu wanda ya kusan shekaru 40 suna fafatawa a tsakaninsu.

Kasashen biyu sun yi yaki na karshe a tsakaninsu kan mallakar yankin Karabakh a shekara ta 2020 haka ma sun tabka yake-yake a kan malakar yankin a shekaru 1990 da bayansa, har zuwa lokacinda Azerbaijan ta kwace yankin a cikin sa,o,ii a yankin 2020. Sannan Armenia ta sallama mata yankin. Kasashen duniya dai sun amince da cewa yankin na Azerbaijan ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted